6
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji. Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba. Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci. Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.
“Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa. Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”
Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.
10 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, 11 “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”
12 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”
Asalin iyalin Musa da Haruna
13 Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.
 
14 Waɗannan su ne shugabannin iyalansu.*
 
’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne,
Hanok da Fallu, Hezron da Karmi.
Waɗannan su ne dangin Ruben.
 
15 ’Ya’yan Simeyon maza su ne,
Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
Waɗannan su ne dangin Simeyon.
 
16 Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta,
Gershon, Kohat da Merari.
Lawi ya yi shekara 137.
17 ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne,
Libni da Shimeyi.
18 ’Ya’yan Kohat maza, su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
Kohat ya yi shekara 133.
19 ’Ya’yan Merari maza, su ne,
Mali da Mushi.
Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.
 
20 Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa.
Amram ya yi shekara 137.
21 ’Ya’yan Izhar maza, su ne,
Kora, Nefeg da Zikri.
22 ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne,
Mishayel, Elzafan da Sitri.
23 Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.
 
24 ’Ya’yan Kora maza, su ne,
Assir, Elkana da Abiyasaf.
Waɗannan su ne dangin Kora.
 
25 Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas.
 
Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.
 
26 Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.” 27 Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.
Haruna zai yi magana a madadin Musa
28 Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar, 29 ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”
30 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”
* 6:14 Ibraniyanci yana da iyalai ne a nan, aya 25 kuma yana kwatanta babbar ƙungiya fiye da dangi ne.