1 Tessalonikawa
1
1 Bulus, Sila da Timoti,
Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.
Alheri da salama su kasance tare da ku.
Godiya saboda bangaskiyar Tessalonikawa
2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu.
3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
4 Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku,
5 domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.
6 Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.
7 Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.
8 Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai,
9 gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya,
10 ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.