9
Sujada a cikin tabanakul na duniya
1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.
2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.
3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,
4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.
5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.
6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.
7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.
8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.
9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.
10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.
Jinin Kiristi
11 Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.
12 Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.
13 In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
14 balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.
16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,
17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.
18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.
19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.
20 Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”
21 Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.
22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
23 Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.
24 Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
25 Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.
26 Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.
27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,
28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.