14
Tuba don kawo albarka
1 Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku.
Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!
2 Ku ɗauki magana tare da ku
ku komo wurin Ubangiji.
Ku ce masa,
“Ka gafarta mana dukan zunubanmu
ka kuma karɓe mu da alheri,
don mu iya yabe ka da leɓunanmu.
3 Assuriya ba za su iya cece mu ba;
ba za mu hau dawakan yaƙi ba.
Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’
wa abin da hannuwanmu suka yi ba,
gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”
4 “Zan gyara ɓatancinsu
in kuma ƙaunace su a sake,
gama fushina ya juya daga gare su.
5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila
zai yi fure kamar lili.
Kamar al’ul na Lebanon
zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;
6 tohonsa za su yi girma.
Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun,
ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.
7 Mutane za su sāke zauna a inuwarsa.
Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi.
Zai yi fure kamar kuringa,
zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.
8 Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka?
Zan amsa masa in kuma lura da shi.
Ni kamar koren itacen fir ne;
amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”
9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.
Hanyoyin Ubangiji daidai ne;
masu adalci sukan yi tafiya a kansu,
amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.