3
Sulhun Hosiya da matarsa
1 Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”
2 Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir.
3 Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare da ke.”
4 Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki.
5 Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe.