5
Hukunci a kan Isra’ila
“Ku ji wannan, ku firistoci!
Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa!
Ku saurara, ya ku gidan sarauta!
Wannan hukunci yana a kanku,
kun zama tarko a Mizfa,
ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.
’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla.
Zan hore su duka.
Na san Efraim ƙaf;
Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba.
Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci;
Isra’ila ta lalace.
 
“Ayyukansu ba su ba su dama
su koma ga Allahnsu ba.
Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu;
ba su yarda da Ubangiji ba.
Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu;
Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu;
Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.
Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu
don su nemi Ubangiji,
ba za su same shi ba;
ya janye kansa daga gare su.
Su marasa aminci ne ga Ubangiji;
suna haihuwar shegu.
Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu
za su cinye su da gonakinsu.
 
“Amon kakaki a Gibeya,
ƙaho a Rama.
Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen;
ku ja gaba, ya Benyamin.
Efraim za tă zama kango
a ranar hukunci.
A cikin kabilan Isra’ila
na yi shelar abin da yake tabbatacce.
10 Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda
suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne.
Zan zubo musu da fushina a kansu
kamar rigyawar ruwa.
11 An danne Efraim,
an murƙushe ta a shari’a
ta ƙudura ga bin gumaka.
12 Na zama kamar asu ga Efraim,
kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.
 
13 “Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa,
Yahuda kuwa miyakunta,
sai Efraim ya juya ga Assuriya,
ya aika wurin babban sarki don neman taimako.
Amma bai iya warkar da kai ba,
bai iya warkar da miyakunka ba.
14 Gama zan zama kamar zaki ga Efraim,
kamar babban zaki ga Yahuda.
Zan yage su kucu-kucu in tafi;
zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.
15 Sa’an nan zan koma wurina
sai sun yarda da laifinsu.
Za su kuma nemi fuskata;
cikin azabansu za su nace da nemana.”