38
Ciwon Hezekiya
(2 Sarakuna 20.1-11; 2 Tarihi 32.24-26)
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
2 Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
3 “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,
5 “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.
6 Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
7 “ ‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari.
8 Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’ ” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.
9 Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.
10 Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata
dole in bi ta ƙofofin mutuwa
a kuma raba ni da sauran shekaruna?”
11 Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba,
Ubangiji a ƙasa ta masu rai;
ba zan ƙara ga wani mutum,
ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
12 Kamar tentin makiyayi
an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni.
Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata,
ya kuma yanke ni daga sandar saƙa;
dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
13 Na yi jira da haƙuri har safiya,
amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka;
dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
14 Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe,
na yi kuka kamar kurciya mai makoki.
Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai.
Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
15 Amma me zan ce?
Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata.
Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina
saboda wahalar raina.
16 Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa;
ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma.
Ka maido mini da lafiya
ka kuma sa na rayu.
17 Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne
cewa in sha irin wahalan nan.
Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni
daga ramin hallaka;
ka sa dukan zunubaina
a bayanka.
18 Gama kabari ba zai yabe ka ba,
matattu ba za su rera yabonka ba;
waɗanda suka gangara zuwa rami
ba za su sa zuciya ga amincinka ba.
19 Masu rai, masu rai, su suke yabonka,
kamar yadda nake yi a yau;
iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu
game da amincinka.
20 Ubangiji zai cece ni,
za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya
dukan kwanakinmu
a cikin haikalin Ubangiji.
21 Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”
22 Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?”