46
Allolin Babilon
1 Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa;
ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne.
Siffofin da ake yawo da su nawaya ne,
kayan nauyi masu gajiyarwa.
2 Sun durƙusa suka kuma rusuna tare;
ba su iya kuɓutar da nauyin kaya
su kansu sukan tafi bauta.
3 “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,
dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,
ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,
na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura
ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.
Na yi ku zan kuma riƙe ku;
zan lura da ku
in kuma kuɓutar da ku.
5 “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni?
Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?
6 Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka
su kuma auna azurfa a ma’auni;
sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah,
su kuma rusuna su yi masa sujada.
7 Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi;
sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya.
Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba.
Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa;
ba zai iya cetonsa daga wahala ba.
8 “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya,
ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.
9 Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā;
ni ne Allah, kuma babu wani;
ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.
10 Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko,
daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba.
Na ce nufina zai tabbata,
kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
11 Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta;
daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina.
Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru;
abin da na shirya, shi zan aikata.
12 Ku kasa kunne, ku masu taurinkai,
ku da kuke nesa da adalci.
13 Ina kawo adalcina kusa,
ba shi da nisa;
kuma cetona ba zai jinkirta ba.
Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.