48
Isra’ila mai taurinkai
“Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub,
waɗanda ake kira da sunan Isra’ila
suka kuma fito daga zuriyar Yahuda,
ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji
kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila,
amma ba da gaskiya ko adalci ba,
ku da kuke kiran kanku ’yan ƙasar birni mai tsarki
kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni,
bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su;
sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.
Gama na san yadda kuke da taurinkai;
jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne,
goshinku tagulla ne.
Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni;
kafin su faru na yi shelarsu gare ku
saboda kada ku ce,
‘Gumakana ne suka yi su;
siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’
Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka.
Ba za ku yarda da su ba?
 
“Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa,
na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba;
ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba.
Saboda haka ba za ku ce,
‘I, na san da su ba.’
Ba ku ji ko balle ku gane ba;
tun da kunnenku bai buɗu ba.
Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa;
an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa.
Saboda girman sunana na jinkirta fushina;
saboda girman yabona na janye shi daga gare ku,
don dai kada a yanke ku.
10 Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba;
na gwada ku cikin wutar wahala.
11 Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka.
Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina?
Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.
An ’yantar da Isra’ila
12 “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub,
Isra’ila, wanda na kira cewa,
Ni ne shi;
ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.
13 Hannuna ne ya kafa harsashen duniya,
hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai;
sa’ad da na kira su,
duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.
 
14 “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara,
Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa?
Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna
zai aikata nufinsa a kan Babilon;
hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.*
15 Ni kaina, na faɗa;
I, na kira shi.
Zan kawo shi,
zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.
16 “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan.
“Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba;
a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.”
 
Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni,
da Ruhunsa.
 
17 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce,
“Ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau,
wanda ya muku hanyar da za ku bi.
18 Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina,
da salamarku ta zama kamar kogi,
adalcinku kamar raƙuman teku.
19 Da zuriyarku ta zama kamar yashi,
’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa;
da ba za a taɓa yanke sunansu
balle a hallaka su daga gabana ba.”
 
20 Ku bar Babilon,
ku gudu daga Babiloniyawa!
Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki
ku kuma furta shi.
Ku aika shi zuwa iyakokin duniya;
ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”
21 Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada;
ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse;
ya tsage dutse
ruwa kuwa ya kwararo.
 
22 “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.
* 48:14 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 20.