25
Bildad 
 
1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,   
2 “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;  
yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.   
3 Za a iya ƙirga rundunarsa?  
A kan wane ne ba ya haska haskensa?   
4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?  
Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?   
5 In har wata da taurari  
ba su da tsarki a idanunsa,   
6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.  
Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”