15
Itacen inabi da kuma rassa
“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
“Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. 17 Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
Duniya ta ƙi jinin almajirai
18 “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19 Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’*In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21 Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22 Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24 Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25 Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
Aikin Ruhu Mai Tsarki
26 “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. 27 Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.
* 15:20 Yoh 13.16 15:25 Zab 35.19; Zab 69.4