7
Zunubin Akan
Amma Isra’ilawa ba su yi aminci game da kayan da aka hallaka ba; Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera, na kabilan Yahuda ya kwashi waɗansu abubuwa, saboda haka fushin Ubangiji ya sauka a kan Isra’ilawa.
Sai Yoshuwa ya aika mutane daga Yeriko zuwa Ai kusa da Bet-Awen gabas da Betel, ya ce musu, “Ku je ku leƙo ku ga yadda yankin yake.” Sai mutanen suka je suka leƙo asirin ƙasar Ai.
Da suka dawo wurin Yoshuwa suka ce, “Ba lalle dukan jama’a su je yaƙi da Ai ba, ka aika mutum dubu biyu ko dubu uku su je su ciwo ƙasar da yaƙi, ba sai ka dami mutane duka ba, gama mutanen wurin kaɗan ne.” Saboda haka sai kimanin mutum duba uku suka haura; amma mutanen Ai suka fatattake su, suka kashe Isra’ilawa wajen mutum talatin da shida, suka fafari Isra’ilawa tun daga bakin ƙofar birnin har zuwa wurin da ake fasa duwatsu. Suka karkashe su a gangare. Wannan ya sa zuciyar Isra’ilawa ta narke suka zama kamar ruwa.
Sai Yoshuwa ya yaga tufafinsa ya fāɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, yana can har yamma. Dattawan Isra’ila ma suka yi haka, suka zuba toka a kawunansu. Yoshuwa kuma ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, me ya sa ka sa mutanen nan suka ƙetare Urdun don ka bari mu shiga hannun Amoriyawa su hallaka mu? Kila da mun haƙura mun zauna a ɗaya gefen Urdun da ya fi mana! Ya Ubangiji me zan ce, yanzu da abokan gāban Isra’ilawa suka ci ƙarfinsu? Yanzu Kan’aniyawa da sauran jama’a za su ji, za su zo su kewaye mu su share sunanmu daga duniya. To, yanzu me za ka yi don girman sunanka?”
10  Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka tashi! Me kake yi kwance rubda ciki? 11 Isra’ilawa sun yi zunubi, sun karya sharaɗin da na yi musu. Sun ɗauki waɗansu abubuwan da aka keɓe; sun yi sata, sun yi ƙarya, sun ɓoye su cikin kayansu. 12 Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka.
13 “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.
14 “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum. 15 Mutumin da aka same shi da haramtattun abubuwan kuwa za a ƙone shi, duk da mallakarsa domin ya karya sharaɗin da Ubangiji ya yi muku, ya yi abin kunya a Isra’ila!’ ”
16 Kashegari da sassafe Yoshuwa ya sa Isra’ilawa suka fito kabila-kabila, aka ware kabilar Yahuda. 17 Gidan Yahuda suka zo gaba, sai aka ware gidan Zera, aka sa suka fito iyali-iyali, sai aka ware Zabdi. 18 Yoshuwa kuwa ya sa iyalin Zabdi suka fito mutum-mutum, sai kuwa aka ware Akan ɗan Karmi, ɗan Zimri, ɗan Zera na kabilar Yahuda.
19 Sai Yoshuwa ya ce wa Akan, “Ɗana, sai ka ba Ubangiji, Allah na Isra’ila ɗaukaka, ka yi masa yabo. Ka gaya mini abin da ka yi; kada ka ɓoye mini.”
20 Akan kuwa ya amsa ya ce, “Gaskiya ne! Na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi. 21 A cikin ganimar, na ga doguwar riga mai kyau irin ta Babilon, da shekel ɗari biyu na azurfa, da kuma sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai raina ya so su, na kuwa kwashe su. Na tona rami a cikin ƙasa a tentina; na ɓoye.”
22 Sai Yoshuwa ya aiki ’yan aika suka tafi da gudu zuwa tenti ɗin, haka kuwa suka same su a ɓoye a tentinsa, da azurfa a ƙarƙashi. 23 Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji.
24 Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor. 25 Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.”
Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran. 26 Suka tara manyan duwatsu a kan Akan, tarin duwatsun na nan a can har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga fushinsa mai zafi. Saboda haka ake kiran wurin Kwarin Akor.