Luka
1
Gabatarwa
Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu, kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai.
An yi faɗar haihuwar Yohanna Mai Baftisma
A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.
Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah, sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare. 10 Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a.
11 Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare. 12 Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa. 16 Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu. 17 Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”
18 Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”
19 Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. 20 Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”
21 Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. 22 Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.
23 Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. 24 Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. 25 Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”
Annabcin haihuwar Yesu
26 A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, 27 gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. 28 Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.”
29 Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka? 30 Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. 31 Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. 32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, 33 zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”
34 Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”
35 Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi* Ɗan Allah. 36 ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. 37 Gama ba abin da zai gagari Allah.”
38 Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa.
Maryamu ta ziyarci Elizabet
39 A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, 40 inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. 41 Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42 Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43 Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? 44 Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45 Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”
Waƙar Maryamu
46 Sai Maryamu ta ce,
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,
daga zamani zuwa zamani.
51 Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;
ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.
52 Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu
amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53 Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa
amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54 Ya taimaki bawansa Isra’ila,
yana tunawa yă nuna jinƙai
55 ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,
kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”
56 Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.
Haihuwar Yohanna Mai Baftisma
57 Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58 Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
59 A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60 amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”
61 Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”
62 Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63 Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64 Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. 65 Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. 66 Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.
Waƙar Zakariya
67 Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,
68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69 Ya tā mana ƙahon ceto
a gidan bawansa Dawuda
70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu
daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu
72 don yă nuna jinƙai ga kakanninmu,
yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73 rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,
74 don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,
yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75 cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.
 
 
76 “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;
gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
77 don ka sanar da mutanensa ceto,
ta wurin gafarar zunubansu,
78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,
hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,
79 don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,
da kuma cikin inuwar mutuwa,
don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”
80 Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.
* 1:35 Ko kuwa Saboda haka, yaron da za a haifa za a kira shi mai tsarki