21
Bayarwar gwauruwa
(Markus 12.41-44)
1 Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin.
2 Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu.
3 Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran.
4 Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”
Alamun ƙarshen zamani
(Mattiyu 24.1,2; Markus 13.1,2)
5 Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,
6 “Wannan abin da kuke kallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowannensu, za a rushe shi.”
(Mattiyu 24.3-14; Markus 13.3-13)
7 Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za tă nuna cewa suna dab da faruwa?”
8 Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.
9 Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
10 Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki.
11 Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.
12 “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.
13 Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.
14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.
15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.
16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.
17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.
18 Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.
19 Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
(Mattiyu 24.15-21; Markus 13.14-19)
20 “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.
21 A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.
22 Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.
23 Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.
24 Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.
(Mattiyu 24.29-31; Markus 13.24-27)
25 “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.
26 Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.
27 A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.
28 Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”
(Mattiyu 24.32-35; Markus 13.28-31)
29 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.
30 A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.
31 Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.
32 “Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.
33 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
34 “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.
35 Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.
36 Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”
37 Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun.
38 Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi.