5
Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu;
duba, ka ga kunyar da muka sha.
An ba wa baƙi gādonmu,
gidajenmu kuma aka ba bare.
Mun zama marayu marasa ubanni,
uwayenmu kamar gwauraye.
Dole mu sayi ruwan da muke sha;
sai mun biya mu sami itace.
Masu fafararmu sun kusa kama mu;
mun gaji kuma ba dama mu huta.
Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya
don mu sami isashen abinci.
Kakanninmu sun yi zunubi
kuma ba sa nan yanzu,
mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.
Bayi suna mulki a kanmu,
kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu.
Muna samun burodi a bakin rayukanmu
domin takobin da yake a jeji.
10 Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,
muna jin zazzaɓi domin yunwa.
11 An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona,
da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.
12 An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu;
ba a ba wa dattawa girma.
13 Samari suna faman yin niƙa;
yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.
14 Dattawan sun bar ƙofar birnin,
samari sun daina rera waƙa.
15 Farin ciki ya rabu da zuciyarmu;
rayuwarmu ta zama makoki.
16 Rawani ya fāɗi daga kanmu.
Kaiton mu gama mun yi zunubi!
17 Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi;
domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe
18 gama Tudun Sihiyona ya zama kufai,
sai diloli ke yawo a wurin.
 
19 Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada;
kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
20 Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe?
Me ya sa ka yashe mu da jimawa?
21 Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo;
ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā
22 sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya
kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.