10
Mutuwar Nadab da Abihu
’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji. Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce,
“ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni
za a tabbata ni mai tsarki ne;
a fuskar dukan mutane
za a kuwa girmama ni.’ ”
Haruna ya yi shiru.
Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.” Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.
Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai,* kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa.
Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. 10 Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, 11 za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”
12 Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. 13 Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni. 14 Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa. 15 Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
16 Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar, ’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya, 17 “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji. 18 Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.”
19 Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?” 20 Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu.
* 10:6 Ko kuwa Kada ku buɗe kawunanku