19
Dokoki iri-iri
Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.
“ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
“ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.
“ ‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku. Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi. In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba. Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa.
“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. 10 Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
11 “ ‘Kada ku yi sata.
“ ‘Kada ku yi ƙarya.
“ ‘Kada ku ruɗe juna.
12 “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
13 “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace.
“ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
14 “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
15 “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
16 “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku.
“ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
17 “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
18 “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
19 “ ‘Ku kiyaye farillaina.
“ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara.
“ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku.
“ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
20 “ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba. 21 Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji. 22 Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
23 “ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci.* Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba. 24 A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji. 25 Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
26 “ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa.
“ ‘Kada ku yi duba ko sihiri.
27 “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
28 “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
29 “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
30 “ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.
31 “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
32 “ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
33 “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi. 34 Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
37 “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ”
* 19:23 Da Ibraniyanci marasa kaciya