5
An yi alkawarin mai mulki daga Betlehem
1 Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,
gama an kewaye mu da yaƙi.
Za su bugi kumatun mai mulkin
Isra’ila da sandar ƙarfe.
2 “Amma ke, Betlehem ta Efrata,
ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda,
daga cikinki wani zai zo domina
wanda zai yi mulkin Isra’ila,
wanda asalinsa
tun fil azal ne.”
3 Saboda haka za a yashe Isra’ila
har sai wadda take naƙuda ta haihu
sauran ’yan’uwansa kuma sun dawo
su haɗu da Isra’ilawa.
4 Zai tsaya yă yi kiwon garkensa
da ƙarfin Ubangiji,
cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.
Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa
za tă kai har ƙarshen duniya.
5 Zai kuma zama salamarsu.
Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari
suka tattake kagarunmu,
za mu tā da makiyaya bakwai,
har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.
6 Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi,
ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.
Zai cece mu daga hannun Assuriyawa
sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari
suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.
7 Raguwar Yaƙub za tă kasance
a tsakiyar mutane masu yawa
kamar raɓa daga Ubangiji,
kamar yayyafi a kan ciyawa,
wanda ba ya jiran mutum
ko kuma yă dakata wa ɗan adam.
8 Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,
a cikin mutane masu yawa,
kamar zaki a cikin sauran namun jeji,
kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,
wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,
ba kuwa wanda zai cece su.
9 Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,
za a hallaka maƙiyanka duka.
10 “A wannan rana,” in ji Ubangiji
“Zan hallaka dawakanku daga cikinku,
in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.
11 Zan hallaka biranen ƙasarku
in yi rugu-rugu da dukan katangunku.
12 Zan kawar da maitarku,
ba za a ƙara yin sihiri ba.
13 Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa
da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,
nan gaba ba za ku ƙara rusuna
wa aikin hannuwanku ba.
14 Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku
in kuma rurrushe biranenku.
15 Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala
a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”