3
“Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki. Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci. Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya.
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Keta alkawari ta wurin ƙin fid da zakka
“Ni Ubangiji ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba. Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’
“Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi.
“Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’
“A wajen zakka da hadayu. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. 10 Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. 11 Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 12 “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
13 “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji.
“Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’
14 “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki? 15 A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”
16 Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
17 “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata*, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. 18 Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
* 3:17 Ko kuwa Maɗaukaki, “ajiyayyen mallakata, a ranar da na aikata”