8
1 sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila.
2 Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta.
3 Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.
4 Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.
5 Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye.
6 Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.
7 Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can.
8 Suka karanta daga Littafin Dokar Allah, suna sa kowa ya gane, suna kuma ba da fassarar domin mutane su fahimci abin da ake karatu.
9 Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.
10 Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”
11 Lawiyawa suka rarrashi mutane duka suna cewa, “Ku natsu, gama wannan rana ce mai tsarki. Kada ku yi baƙin ciki.”
12 Sa’an nan dukan mutane suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci, gama yanzu sun fahimci kalmomin da aka karanta musu.
13 A rana ta biyu ga wata, shugabannin iyalai, tare da firistoci da Lawiyawa, suka taru kewaye da Ezra malamin Doka don su mai da hankali ga kalmomin Dokar.
14 Suka tarar a rubuce a cikin Doka wadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa, cewa Isra’ilawa su zauna a bukkoki a lokaci bikin watan bakwai
15 kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce.
16 Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim.
17 Dukan jama’ar da suka komo daga zaman bauta suka yi bukkoki suka kuma zauna a cikinsu. Daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har yă zuwa yau, Isra’ilawa ba su taɓa yin bikinsa haka ba. Mutane suka cika da farin ciki sosai.
18 Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.