24
1 To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.
2 Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,
3 sai ya yi annabcinsa ya ce,
“Maganar Bala’am ɗan Beyor,
saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,
4 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,
maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki,
mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.
5 “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub,
wuraren zamanka, ya Isra’ila!
6 “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe,
kamar lambu kusa da rafi,
kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,
kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.
7 Ruwa zai kwararo daga bokitinsu;
irinsu za su sami ruwa a yalwace.
“Sarkinsu zai fi sarkin Agag;
mulkinsu zai ɗaukaka.
8 “Allah ya fitar da su daga Masar;
suna da ƙarfin kutunkun ɓauna.
Sun cinye abokan gāban,
suka kakkarya ƙasusuwansu;
da kibiyoyinsu suka sossoke su.
9 Kamar zaki sun laɓe sun kwanta,
kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su?
“Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka
waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”
10 Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.
11 Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”
12 Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,
13 ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?
14 Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”
Maganar Bala’am ta huɗu na abin da Allah ya faɗa
15 Sa’an nan ya furta saƙonsa.
“Maganar Bala’am ɗan Beyor,
saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,
16 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,
wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka,
wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki,
wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.
17 “Na gan shi, amma ba yanzu ba;
na hange shi, amma ba kusa ba.
Tauraro zai fito daga Yaƙub;
sandan mulki zai fito daga Isra’ila.
Zai ragargaje goshin Mowab,
kawunan dukan ’ya’yan Set.
18 Za a ci Edom da yaƙi;
za a ci Seyir, abokiyar gābanta,
amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi.
19 Mai mulki zai fito daga Yaƙub
yă hallaka waɗanda suka ragu a birnin.”
Maganar Bala’am ta ƙarshe na abin da Allah ya faɗa
20 Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa.
“Amalek yana cikin al’ummai na fari,
amma zai zama na ƙarshen da za a hallaka.”
21 Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa.
“Wurin zamanku lafiya yake,
an kuma sa sheƙarku a cikin duwatsu;
22 duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa
sa’ad da Asshur ya kame ku.”
23 Sai ya furta maganarsa ya ce,
“Wayyo, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi haka?
24 Jiragen ruwa za su zo daga Kittim;
za su murƙushe Asshur da Eber,
amma su ma za a hallaka su.”
25 Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.