16
Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,
amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
 
Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi,
amma Ubangiji yakan auna manufofi.
 
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
 
Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa,
har ma da mugaye domin ranar masifa.
 
Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai.
Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
 
Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi;
ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
 
Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji,
yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.
 
Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci
da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.
 
’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,
amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
 
10 Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah,
kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba.
 
11 Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne;
dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
 
12 Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau,
gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.
 
13 Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya;
sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.
 
14 Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne,
amma mai hikima yakan faranta masa rai.
 
15 Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan;
tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
 
16 Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,
ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
 
17 Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta;
duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.
 
18 Girmankai yakan zo kafin hallaka,
girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.
 
19 Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai,
da ka raba ganima da masu girman kai.
 
20 Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,
kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.
 
21 Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai,
kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.
 
22 Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi,
amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.
 
23 Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa,
kuma leɓunansa kan inganta umarni.
 
24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,
mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
 
25 Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum,
amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
 
26 Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki;
yunwarsa kan sa ya ci gaba.
 
27 Mutumin banza yakan ƙulla mugunta,
kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna.
 
28 Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali,
mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
 
29 Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa
ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.
 
30 Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce;
duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan.
 
31 Furfura rawani ne mai daraja;
akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
 
32 Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,
ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
 
33 Akan jefa ƙuri’a a kan cinya,
amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.