21
A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne
wanda yake bi da shi duk inda ya so.
 
Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke,
amma Ubangiji yakan auna zuciya.
 
Yin abin da yake daidai da kuma nagari
Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
 
Girmankai da fariya,
su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
 
Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba
in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
 
Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya
tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
 
Rikicin mugaye zai yi gāba da su,
gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
 
Hanyar mai laifi karkatacciya ce,
amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
 
Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki
da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
 
10 Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta;
maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
 
11 Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo;
sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
 
12 Mai Adalci kan lura da gidan mugu
kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
 
13 In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci,
shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
 
14 Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi,
kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
 
15 Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci
amma fargaba ga masu aikata mugunta.
 
16 Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi
kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
 
17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci;
duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
 
18 Mugu kan zama abin fansa don adali,
marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
 
19 Gara a zauna a hamada
da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
 
20 A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau,
amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
 
21 Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna
kan sami rai, wadata da girmamawa.
 
22 Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa
ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
 
23 Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa
kan kiyaye kansa daga masifa.
 
24 Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa;
yana yin abubuwa da girmankai ainun.
 
25 Marmarin rago zai zama mutuwarsa,
domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
26 Dukan yini yana marmari ya sami ƙari,
amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
 
27 Hadayar mugaye abin ƙyama ne,
balle ma in aka kawo da mugun nufi!
 
28 Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka,
kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.*
 
29 Mugun mutum kan yi tsayin daka,
amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
 
30 Babu hikima, babu tunani, babu shirin
da zai yi nasara a kan Ubangiji.
 
31 Akan shirya doki domin ranar yaƙi,
amma nasara tana ga Ubangiji ne.
 
* 21:28 Ko kuwa / amma kalmomin mai biyayya za su ci gaba da kasancewa