23
Faɗi 7
Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki,
ka lura sosai da abin da yake gabanka,
ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka
in kai mai ci da yawa ne.
Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi
gama wannan abinci ruɗu ne.
Faɗi 8
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki;
ka kasance da hikimar dainawa.
Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace,
gama tabbatacce sukan yi fikafikai
sukan tashi sama kamar gaggafa.
Faɗi 9
Kada ka ci abincin mai rowa,
kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;
gama shi wani irin mutum ne
wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin.*
Zai ce maka, “Ci ka sha,”
amma zuciyarsa ba ta tare da kai.
Za ka yi amai ɗan abin da ka ci
dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.
Faɗi 10
Kada ka yi magana da wawa,
gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.
Faɗi 11
10 Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā
ko ka ɗiba gonar marayu,
11 gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi;
zai kuwa yi magana dominsu.
Faɗi 12
12 Ka mai da hankali ga umarni
ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.
Faɗi 13
13 Kada ka bar yaro ba horo;
in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
14 Ka hukunta shi da sanda
ka ceci ransa daga mutuwa.
Faɗi 14
15 Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce,
to, zuciyata za tă yi murna;
16 cikin cikina zai yi farin ciki
in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.
Faɗi 15
17 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi,
amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
18 Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
Faɗi 16
19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,
ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.
20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa
ko masu haɗama kansu da abinci,
21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,
gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
Faɗi 17
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
ka nemi hikima, horo da fahimi.
24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;
duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;
bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
Faɗi 18
26 Ɗana, ka ba ni zuciyarka
bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
27 gama karuwa rami ne mai zurfi
mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.
28 Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira
tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.
Faɗi 19
29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki?
Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni?
Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?
30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi,
waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.
31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja,
sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya,
sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!
32 A ƙarshe yana sara kamar maciji
da kuma dafi kamar gamsheƙa.
33 Idanunka za su riƙa gane-gane,
zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.
34 Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna,
kwance a sama itacen jirgin ruwa.
35 Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba!
Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa!
Yaushe zan farka
don in ƙara shan wani?”
* 23:7 Ko kuwa gama yadda yake tunani a cikinsa, haka yake; Ko kuwa gama yadda ya sa a bikin, haka yake