5
Gargaɗi a kan zina
Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata
ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
don ka ci gaba da yin kome daidai
leɓunanka za su adana sani.
Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,
maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,
mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;
sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
Ba ta wani tunanin rayuwa;
hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
 
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
kada ku juye daga abin da nake faɗa.
Ku yi nesa da hanyarta,
kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu
da kuma shekarunku ga wani marar imani,
10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku
wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,
sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
12 Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo!
Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
13 Ban yi biyayya da malamaina ba
ko in saurari masu koyar da ni.
14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya
a tsakiyar dukan taron.”
 
15 Ku sha ruwa daga tankinku,
ruwa mai gudu daga rijiyarku.
16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,
rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?
17 Bari su zama naka kaɗai,
don kada ka raba da baƙi.
18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,
bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,
bari mamanta su ishe ka kullum,
bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?
Don me za ka rungume matar wani?
 
21 Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji,
yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
22 Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi;
igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
23 Zai mutu saboda rashin ɗa’a
yawan wawancinsa zai sa yă kauce.