Zabura 29
Zabura ta Dawuda.
Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,
ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
 
Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,
Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.
Muryar Ubangiji mai iko ce;
muryar Ubangiji da girma take.
Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.
Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,
Siriyon* kuma kamar ɗan jakin jeji.
Muryar Ubangiji ta buga
da walƙatar walƙiya.
Muryar Ubangiji ta girgiza hamada
Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.
Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak
ya kakkaɓe itatuwan kurmi.
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
 
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;
Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.
* Zabura 29:6 Wato, Dutsen Hermon Zabura 29:9 Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu.