Zabura 95
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
7 gama shi ne Allahnmu
mu mutanen makiyayansa ne,
garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.
Yau, in kuka ji muryarsa,
8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,
kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,
9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,
ko da yake sun ga abin da na yi.
10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;
na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,
kuma ba su san hanyoyina ba.’
11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,
‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”