10
Shawulu ya ɗauke ransa
(1 Sama’ila 31.1-13)
To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.
Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.”
Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.
Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa. Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu. 10 Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon.
11 Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, 12 sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
13 Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, 14 bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.