14
Gida da iyalin Dawuda
(2 Sama’ila 5.11-16)
1 To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada.
2 Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila.
3 A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin ’ya’yan maza da mata.
4 Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
5 Ibhar, Elishuwa, Elfelet,
6 Noga, Nefeg, Yafiya,
7 Elishama, Beyeliyada da Elifelet.
Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi
(2 Sama’ila 5.17-25)
8 Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su.
9 To, fa, Filistiyawa suka zo suka kai wa Kwarin Refayim hari;
10 sai Dawuda ya roƙi Allah ya ce, “In tafi in yaƙi Filistiyawa? Za ka ba da su gare ni?”
Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ka tafi, zan ba da su gare ka.”
11 Saboda haka Dawuda da mutanensa suka haura zuwa Ba’al-Ferazim, a can kuwa suka ci Filistiyawa da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa kan raraki ƙasa, haka Allah ya raraki abokan gābana ta wurin hannuna.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
12 Filistiyawa suka yashe allolinsu, Dawuda kuma ya ba da umarnai a ƙone su a wuta.
13 Filistiyawa suka sāke kai hari wa kwarin;
14 sai Dawuda ya sāke roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa, “Kada ka tafi kai tsaye, amma ka yi zobe kewaye da su, ka kuma fāɗa musu a gaban itatuwan tsamiya.
15 Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.”
16 Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer.
17 Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa.