20
An ci Rabba
(2 Sama’ila 11.1; 12.26-31)
1 Da bazara, a lokacin da sarakuna kan tafi yaƙi, Yowab ya jagorance mayaƙa. Ya lalatar da ƙasar Ammonawa ya kuma tafi Rabba ya yi mata kwanto, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabba, ya kuma bar ta kango.
2 Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin
3 ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima.
Yaƙi da Filistiyawa
(2 Sama’ila 21.15-22)
4 Ana nan, sai yaƙi ya ɓarke a Gezer tsakanin Isra’ila da Filistiyawa. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar Refahiyawa, ta haka kuma aka ci Filistiyawa da yaƙi.
5 Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa.
6 Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce.
7 Sa’ad da ya yi wa Isra’ila ba’a, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda ya kashe shi.
8 Waɗannan su ne zuriyar Rafa a Gat, Dawuda da mutanensa sun kashe su.