23
Lawiyawa
1 Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.
2 Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa.
3 Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.
4 Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.
5 Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”
6 Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.
Gershon
7 Na Gershonawa,
Ladan da Shimeyi.
8 ’Ya’yan Ladan maza su ne,
Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.
9 ’Ya’yan Shimeyi maza su ne,
Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka.
Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.
10 ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne,
Yahat, Zina, Yewush da Beriya.
Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.
11 Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.
Kohatawa
12 ’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.
13 ’Ya’yan Amram maza su ne,
Haruna da Musa.
Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.
14 An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.
15 ’Ya’yan Musa maza su ne,
Gershom da Eliyezer.
16 Zuriyar Gershom su ne,
Shebuwel ne ɗan fari.
17 Zuriyar Eliyezer su ne,
Rehabiya ne ɗan fari.
Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.
18 ’Ya’yan Izhar maza su ne,
Shelomit ne ɗan fari.
19 ’Ya’yan Hebron maza su ne,
Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
20 ’Ya’yan Uzziyel maza su ne,
Mika na fari da Isshiya na biyu.
Merariyawa
21 ’Ya’yan Merari maza su ne,
Mali da Mushi.
’Ya’yan Mali maza su ne,
Eleyazar da Kish.
22 Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.
23 ’Ya’yan Mushi maza su ne,
Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.
24 Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.
25 Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,
26 Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.”
27 Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye.
28 Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.
29 Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.
30 Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma
31 da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.
32 A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.