26
Matsaran ƙofofi
1 Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne,
Daga Korayawa,
Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza.
2 Meshelemiya yana da ’ya’ya maza.
Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu,
Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
3 Elam na biyar, Yehohanan na shida
da Eliyehoyenai na bakwai.
4 Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza.
Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu,
Yowa na uku, Sakar na huɗu
Netanel na biyar,
5 Ammiyel na shida,
Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas.
(Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)
6 Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
7 ’Ya’yan Shemahiya maza su ne,
Otni, Rafayel, Obed da Elzabad;
danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.
8 Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
9 Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.
10 Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza.
Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),
11 Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku
sai kuma Zakariya na huɗu.
’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.
12 Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.
13 Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.
14 Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya.
Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.
15 Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza.
16 Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa.
Aikin tsaro bisa ga mai tsaro.
17 Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas,
huɗu a ƙofar kudu,
huɗu kuma a ƙofar arewa,
biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.
18 Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin kansa.
19 Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.
Masu ajiya da sauran manyan ma’aikata
20 ’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe.
21 Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli,
22 ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji.
23 Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki.
24 Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali.
25 Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.
26 Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
27 Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.
28 Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.
29 Daga mutanen Izhar,
Kenaniya da ’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila.
30 Daga zuriyar Hebron,
Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.
31 Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu.
A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.
32 Yeriya yana da ’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki.