15
Sauye-sauyen Asa
Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded. Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, “Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku. Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka. Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi. A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa. Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku.”
Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.
Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
10 Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa. 11 A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita. 12 Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu. 13 Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace. 14 Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni. 15 Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.
16 Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. 17 Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa. 18 Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe.
19 Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa.