25
Amaziya sarkin Yahuda
(2 Sarakuna 14.1-6)
1 Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin ce; ita daga Urushalima ne.
2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma ba da dukan zuciyarsa ba.
3 Bayan sarauta ta kahu a ƙarƙashinsa, sai ya kashe hafsoshin da suka kashe mahaifinsa sarki.
4 Duk da haka bai kashe ’ya’yansu maza ba amma ya yi bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Doka, a cikin Littafin Musa, inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda ’ya’yansu ba; ba kuwa za a kashe ’ya’ya saboda iyayensu ba; kowa zai mutu saboda zunubansa ne.”
(2 Sarakuna 14.7)
5 Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa.
6 Ya kuma ɗauko sojan haya jarumawa dubu ɗari ɗaya daga Isra’ila a kan talenti ɗari na azurfa.
7 Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, waɗannan runduna daga Isra’ila ba za su tafi tare da kai ba, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, ba ya nan da wani cikin mutanen Efraim.
8 Ko da ma ya tafi ya yi faɗa da ƙwazo a cikin yaƙi, Allah zai tumɓuke shi a gaban abokan gāba, gama Allah yana da iko yă taimaka ko yă tumɓuke.”
9 Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?”
Mutumin Allah ya amsa, “Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.”
10 Saboda haka Amaziya ya sallame rundunonin da suka zo daga Efraim, ya kuma mayar da su gida. Suka husata da Yahuda suka koma gida da fushi sosai.
11 Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma.
12 Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca.
13 Ana cikin haka, sai rundunar da Amaziya ya mai da su gida, waɗanda ba a bari suka tafi yaƙin ba, suka kai wa garuruwan Yahuda daga Samariya zuwa Bet-Horon hari. Suka kashe mutane dubu uku suka kwashe ganima mai yawan gaske.
14 Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa.
15 Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?”
16 Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?”
Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
(2 Sarakuna 14.8-14)
17 Bayan Amaziya sarkin Yahuda ya nemi shawara mashawartansa, sai ya kalubalanci Yowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, “Zo mu gamu fuska da fuska.”
18 Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar.
19 Ka ce wa kanka cewa ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana fariya da ɗaga kai. Amma tsaya dai a gida! Me ya sa kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da ta Yahuda?”
20 Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.
21 Saboda haka Yowash sarkin Isra’ila ya kai yaƙi. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh a Yahuda.
22 Isra’ila ta fatattaki Yahuda, sai kowane mutum ya gudu zuwa gidansa.
23 Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida.
24 Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
(2 Sarakuna 14.15-20)
25 Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya rayu shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila.
26 Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
27 Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.
28 Aka dawo da shi a kan doki, aka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Yahuda.