30
Hezekiya ya yi Bikin Ƙetarewa
1 Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
2 Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu.
3 Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
4 Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.
5 Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.
6 Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa,
“Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
7 Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.
8 Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.
9 In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”
10 ’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.
11 Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima.
12 Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.
13 Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu.
14 Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.
15 Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
16 Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su.
17 Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba.
18 Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa
19 wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.”
20 Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.
21 Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.
22 Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.
23 Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma.
24 Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu.
25 Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda.
26 Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba.
27 Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.