32
Sennakerib ya yi wa Urushalima barazana
(2 Sarakuna 18.13-37; Ishaya 36.1-22)
1 Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa.
2 Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima,
3 sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.
4 Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?”
5 Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.
6 Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi.
7 “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.
8 Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.
9 Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa,
10 “Ga abin da Sennakerib sarkin Assuriya ya ce ga me kake dogara, har da ka dāge cikin Urushalima da aka yi mata kwanto?
11 Ai, Hezekiya, ruɗinku yake yi, don yă sa ku mutu da yunwa da ƙishirwa sa’ad da yake ce muku, ‘Ubangiji Allahnmu zai cece mu daga hannun sarkin Assuriya.’
12 Hezekiya kansa bai rushe waɗannan masujadan kan tudu da bagadai, yana ce wa Yahuda da Urushalima, ‘Dole ku yi sujada a gaban bagade guda ku kuma ƙone hadayu a kansa ba’?
13 “Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne?
14 Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?
15 Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”
16 Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.
17 Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”
18 Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.
19 Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.
(2 Sarakuna 19.14-19,35-37; Ishaya 37.14-20; 37.36-38)
20 Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan.
21 Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi.
22 Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe.
23 Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi.
Girmankai, nasara da kuma mutuwar Hezekiya
(2 Sarakuna 20.1-11; Ishaya 38.1-8)
24 A kwanakin nan Hezekiya ya yi ciwo, ya yi kusan mutuwa. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wanda ya amsa masa ya kuma ba shi alama.
25 Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima.
26 Sai Hezekiya ya tuba daga girma kan zuciyarsa, haka ma mutanen Urushalima; saboda haka fushin Ubangiji bai zo a kansu a kwanakin Hezekiya ba.
(2 Sarakuna 20.12-19; Ishaya 39.1-8)
27 Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa.
28 Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki.
29 Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai.
30 Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi.
31 Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.
(2 Sarakuna 20.20,21)
32 Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
33 Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.