11
Ragowar Isra’ila
1 To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.
2 Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce,
3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”?
4 Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”
5 Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.
6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7 To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare,
8 kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Allah ya ba su ruhun ruɗewa,
idanu don su kāsa gani,
da kuma kunnuwa don su kāsa ji,
har yă zuwa yau.”
9 Dawuda kuma ya ce,
“Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko,
sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.
10 Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani,
bayansu kuma yă tanƙware har abada.”
Rassan aure
11 Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.
12 Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!
13 Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa,
14 da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.
15 Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba?
16 In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.
17 In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
18 kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.
19 To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”
20 Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.
21 Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.
23 In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.
24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
Dukan Isra’ila za su tsira
25 Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.
26 Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Mai ceto zai zo daga Sihiyona;
zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
27 Wannan kuwa shi ne alkawarina da su
sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”
28 Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,
29 gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.
30 Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,
31 haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.
32 Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.
Ɗaukakawa
33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!
Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,
hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?
Ko kuwa yă ba shi shawara?”
35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,
da Allah zai sāka masa?”
36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.