7
Misali daga aure
Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai. Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.
Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.
Yin fama da zunubi
Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”* Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. 10 Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.
11 Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni. 12 Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.
13 Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.
14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.
21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!
Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
* 7:7 Fit 20.17; M Sh 5.21 7:18 Ko kuwa jikina