12
Mace da ƙaton maciji
1 Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta.
2 Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa.
3 Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa.
4 Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.
5 Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa.
6 Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.
7 Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani.
8 Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama.
9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.
10 Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa,
“Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu,
da kuma ikon Kiristinsa.
Gama mai zargin ’yan’uwanmu,
wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana,
an jefar da shi ƙasa.
11 Sun ci nasara a kansa
ta wurin jinin Ɗan Ragon
da ta wurin kalmar shaidarsu;
ba su ƙaunaci rayukansu sosai
har da za su ja da baya daga mutuwa.
12 Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai,
da ku da kuke zaune a cikinsu!
Amma kaiton duniya da kuma teku,
gama Iblis ya sauko gare ku!
Ya cika da fushi,
domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”
13 Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji.
14 Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.
15 Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya.
16 Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa.
17 Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.