21
Dawuda a Nob
1 Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”
2 Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni.
3 Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.”
4 Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”
5 Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”
6 Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.
7 A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.
8 Dawuda ya ce wa Ahimelek, “Ba ka da māshi ko takobi a nan? Ban kawo māshina ko wani makami ba gama saƙon sarki ya zo mini da gaggawa.”
9 Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.”
Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”
Dawuda a Gat
10 A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat.
11 Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa,
“Shawulu ya kashe dubbai,
Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”
12 Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai.
13 Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa.
14 Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina?
15 Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?”