17
1 Ahitofel ya ce wa Absalom, “Zan zaɓi mutum dubu goma sha biyu su fita a daren nan in fafari Dawuda.
2 Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya. Zan firgita shi, mutanen da suke tare da shi kuwa za su gudu. Sarki ne kaɗai zan kashe
3 in dawo da dukan mutanen a gare ka. Mutuwar wanda kake nema zai zama dawowar duka; dukan mutanen ba za su cutu ba.”
4 Wannan shawara ta gamshi Absalom da dukan dattawan Isra’ila.
5 Amma Absalom ya ce, “A kira mini Hushai mutumin Arkitawan nan shi ma, mu ji abin da zai ce.”
6 Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.”
7 Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau.
8 Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba.
9 Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’
10 Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.
11 “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama.
12 Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai.
13 In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”
14 Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa.
15 Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka.
16 Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ”
17 Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin.
18 Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta.
19 Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.
20 Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?”
Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima.
21 Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.”
22 Saboda haka Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka tashi suka ƙetare Urdun. Kafin wayewar gari, babu wanda ya rage da bai haye ba.
23 Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya hau jakinsa ya koma gidansa a garinsu. Ya kintsa gidansa sa’an nan ya rataye kansa. Ta haka ya mutu, aka kuma binne shi a kabarin mahaifinsa.
24 Dawuda kuwa ya tafi Mahanayim. Absalom kuma ya ƙetare Urdun tare da dukan mutanen Isra’ila.
25 Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab.
26 Isra’ilawa da Absalom suka kafa sansani a ƙasar Gileyad.
27 Sa’ad da Dawuda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lo Debar, da Barzillai mutumin Gileyad daga Rogelim
28 suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,
29 da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu wa Dawuda da mutanensa su ci. Gama sun ce, “Mutanen suna jin yunwa, sun kuma gaji, ga ƙishirwa a hamada.”