Waƙar Waƙoƙi
1
Waƙar Waƙoƙin Solomon.
 
Ƙaunatacciya*
Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa,
gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
Ƙanshin turarenka mai daɗi ne;
sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne.
Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri!
Bari sarki yă kai ni gidansa.
Ƙawaye
Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai,
za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi.
Ƙaunatacciya
Daidai ne su girmama ka!
 
Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa.
Ya ku ’yan matan Urushalima,
ni baƙa ce kamar tentunan Kedar,
kamar labulen tentin Solomon.
Kada ku harare ni domin ni baƙa ce,
gama rana ta dafa ni na yi baƙa.
’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni
suka sa ni aiki a gonakin inabi;
na ƙyale gonar inabi na kaina.
Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka
kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana.
Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe
kusa da garkunan abokanka?
Ƙawaye
Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba,
to, ki dai bi labin da tumaki suke bi
ki yi kiwon ’yan awakinki
kusa da tentunan makiyaya.
Ƙaunatacce
Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya
mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10 ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau,
wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11 Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya,
da adon azurfa.
Ƙaunatacciya
12 Yayinda sarki yake a teburinsa,
turarena ya bazu da ƙanshi.
13 Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni,
kwance a tsakanin ƙirjina.
14 Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni
daga gonakin inabin En Gedi.
Ƙaunatacce
15 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata!
Kai, ke kyakkyawa ce!
Idanunki kamar na kurciya ne.
Ƙaunatacciya
16 Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena!
Kai, kana ɗaukan hankali!
Gadonmu koriyar ciyawa ce.
Ƙaunatacce
17 Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu;
fir su ne katakan rufin gidanmu.
* 1:1 Da farko dai an nuna masu magana ko namiji ko ta mace bisa ga jinsi na wakilan sunayen da Ibraniyanci suka yi amfani da su, a gefen shafi ta wurin salon Ƙaunatacce da Ƙaunatacciya daki-daki. An nuna sauran kalmomin da Abokai. A waɗansu wurare akwai shakka game da ɓangarori da salo. 1:5 Ko kuwa Salma