10
Ubangiji zai lura da Yahuda 
 
1 Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;  
Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.  
Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama  
yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.   
2 Gumaka suna maganganun ruɗu,  
masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,  
suna faɗa mafarkan ƙarya  
suna ba da ta’aziyyar banza.  
Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki  
waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.   
   
 
3 “Ina fushi da makiyayan,  
zan kuma hukunta shugabannin;  
gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura  
da garkensa, wato, gidan Yahuda,  
zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.   
4 Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito,  
daga gare shi za a samu abin kafa tenti,  
daga gare shi za a sami bakan yaƙi,  
daga gare shi za a sami kowane mai mulki.   
5 Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi  
suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi.  
Domin Ubangiji yana tare da su,  
za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.   
   
 
6 “Zan ƙarfafa gidan Yahuda  
in kuma ceci gidan Yusuf.  
Zan maido da su  
domin ina jin tausayinsu.  
Za su zama kamar  
ban taɓa ƙinsu ba,  
gama ni ne Ubangiji Allahnsu  
zan kuma amsa musu.   
7 Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,  
zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.  
’Ya’yansu za su gani su yi murna;  
zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.   
8 Zan ba da alama  
in kuma tattara su.  
Ba shakka zan fanshe su;  
za su yi yawa kamar yadda suke a dā.   
9 Ko da yake na warwatsa su cikin mutane,  
duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni.  
Su da ’ya’yansu za su rayu,  
za su kuwa komo.   
10 Zan komo da su daga Masar  
in kuma tattara su daga Assuriya.  
Zan kawo su Gileyad da Lebanon,  
har wuri yă kāsa musu.   
11 Za su ratsa cikin tekun wahala;  
zan kwantar da raƙuman teku  
dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe.  
Za a ƙasƙantar da Assuriya,  
sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.   
12 Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji  
kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,”  
in ji Ubangiji.