2
Mutum riƙe da ma’auni
Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa! Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?”
Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”
Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta. Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji.
“Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji.
“Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!” Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne. Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni.
10 “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji. 11 “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. 12  Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima. 13 Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.”