5
Naɗaɗɗen littafi mai firiya
Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana!
Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.”*
Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”
Mace a cikin kwando
Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.”
Na tambaya na ce, “Mene ne?”
Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.” Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin mutanen a duk fāɗin ƙasar.”
Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune! Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse.
Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama.
10 Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?”
11 Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya§ don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.”
* 5:2 Da Ibraniyanci tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu goma (tsawonsa wajen mita 9, fāɗinsa kuma wajen mita huɗu da rabi). 5:6 Da Ibraniyanci efa ne; haka ma a ayoyi 7-11. 5:6 ko kuwa bayyanuwar § 5:11 Da Ibraniyanci Shinar. Shinar tsohon sunan Babilon ne. Bisa ga Far 11, a wurin ne mutanen dā suka gina gini mai tsayi na saɓo ga Allah, wanda Ubangiji ya sauka ya dagula harsunansu.