6
1 haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah.
2 Domin ya ce, “A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku.” Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto.
3 Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani.
4 Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala,
5 duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa,
6 cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna.
7 Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu.
8 Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne.
9 Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba.
10 Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai.
11 Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke.
12 Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu.
13 Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku.
14 Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu?
15 Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya?
16 ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: ''Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”
17 Sabili da haka, ''Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu,'' in ji Ubangiji. ''Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku.
18 Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni,'' in ji Ubangiji Mai iko duka.