Afisawa
1
1 Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu.
2 Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu.
4 Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa.
5 Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so.
6 Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa.
7 Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa.
8 Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta.
9 Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu.
10 Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu.
11 An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa.
12 Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu.
13 A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
14 Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne.
15 Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa.
16 Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina.
17 Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa.
18 Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa.
19 Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne.
20 Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai.
21 Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa.
22 Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya.
23 Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.