5
1 Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima.
2 To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar.
3 Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin [suna jira a dama ruwan].
4 Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita.
5 Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas.
6 Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, “ Ko kana so ka warke?”
7 Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, “Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni.”
8 Yesu ya ce masa,” Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi.”
9 Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce.
10 Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba.”
11 Sai ya amsa ya ce, “Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi.”
12 Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?”
13 Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
14 Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”
15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16 To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
17 Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”
18 Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
19 Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
20 Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki.
21 Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa.
22 Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
23 domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
24 Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai.
25 Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.
26 Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa.
27 Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum.
28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa,
29 su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci.
30 Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
31 Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba.
32 Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce.
33 Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya.
34 Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto.
35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan.
36 Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni.
37 Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa.
38 Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
39 Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.
40 kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai.
41 Ba na karbar yabo daga wurin mutane,
42 amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku.
43 Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi.
44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah?
45 Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa.
46 Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni.
47 Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”