10
1 Bayan wadannan abubuwa, Ubangiji ya sake nada wadansu saba'in ya aike su biyu biyu, domin su tafi kowanne birni da wurin da yake niyyan zuwa.
2 Ya ce da su, “Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan sun yi kadan. Saboda haka kuyi addu'a sosai ga Ubangijin girbin, domin ya aiko da ma'aikata cikin gonarsa.
3 Ku tafi, duba na aike ku kamar 'yan raguna cikin kyarkyetai.
4 Kada ku dauki jakan kudi, ko jakar matafiyi, ko takalma, kada ku gai da kowa a kan hanya.
5 Dukan gidan da ku ka shiga, ku fara cewa, 'Bari salama ta kasance a wannan gida.'
6 Idan akwai mutum mai salama a gidan, salamar ku za ta kasance a kansa, amma idan babu, salamar ku za ta dawo wurinku.
7 Ku zauna a wannan gidan, ku ci ku sha abin da suka tanada maku. Gama ma'aikaci ya wajibci ladansa. Kada ku bi gida gida.
8 Dukan birnin da ku ka shiga kuma sun karbe ku, ku ci abin da suka sa a gabanku.
9 Ku warkar da marasa lafiyar da ke wurin. Ku ce da su, 'Mulkin Allah ya zo kusa da ku.'
10 Amma dukan birnin da ku ka shiga, idan ba su karbe ku ba, ku tafi cikin titunansu, ku ce,
11 'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.'
12 Na gaya maku, a ranar shari'a Saduma za ta fi wannan birni samun sauki.
13 Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki.
14 Amma a ranar shari'a Taya da Sidon za su fi ku samun sauki.
15 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani har zuwa sama za a daukaka ki? Babu, za a gangarar dake har zuwa hadas.
16 Wanda ya saurare ku ya saurare ni, wanda ya ki ku, ya ki ni, kuma wanda ya ki ni, ya ki wanda ya aiko ni.”
17 Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, “Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka.”
18 Sai Yesu ya ce masu, “Na ga Shaidan yana fadowa daga sama kamar walkiya.
19 Duba, na ba ku iko ku taka macizai da kunamai, da kuma kan dukan ikon magabci, kuma ba zai iya yin illa a gareku ba ko kadan.
20 Amma duk da haka kada ku yi murna a kan wannan kadai cewa ruhohi suna yi maku biyayya, amma ku yi murna domin an rubuta sunayenku a cikin sama.”
21 Cikin wannan lokacin, ya yi farin ciki kwarai cikin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na ba ka girma, ya Uba, Ubangijin sama da kasa. Domin ka rufe wadannan abubuwa daga masu hikima da ganewa, ka bayyana su ga wadanda ba koyayyu ba ne, kamar kananan yara. I, Uba gama haka ne ya gamshe ka.”
22 Dukan abu, Ubana ya damka su gare ni, kuma babu wanda ya san Dan, sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Dan. Sai kuma wanda Dan ya yi niyyar ya bayyana Uban a gareshi.”
23 Ya juya wajen almajiran, ya ce da su a kadaice, “Masu albarka ne su wadanda suka ga abin da kuke gani.
24 Na fada maku, annabawa da yawa, da sarakuna da yawa sun so da sun ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Kuma sun so da sun ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji su ba.”
25 Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, “Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?”
26 Sai Yesu ya ce masa, “Yaya kake karanta abin da aka rubuta cikin shari'a?”
27 Ya amsa ya ce,”Dole ne ka kaunaci Ubangiji Allah da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka, da dukan lamirinka. Ka kuma kaunaci makwabcinka kamar kanka.”
28 Yesu ya ce ma sa, “Ka amsa daidai, idan ka yi haka za ka rayu.”
29 Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, “To, wanene makwabcina?”
30 Ya amsa ya ce, “Wani mutum yana tafiya daga Urushalima za shi Yariko. Sai ya fada hannun mafasa, suka tube shi, suka kwace dukan abin da ya ke da shi, suka yi masa duka, suka bar shi kamar matacce.
31 Ya zama sai ga wani firist ya na bin wannan hanya, da ya gan shi sai ya bi ta gefe daya ya wuce.
32 Haka kuma sai ga wani Balawi, sa'adda ya zo wurin, ya gan shi sai ya bi ta wani gefe ya wuce shi.
33 Amma wani Basamariye, ya na tafiya sa'adda ya zo wurin da mutumin yake, sa'adda ya ga mutumin sai tausayi ya kama shi.
34 Ya zo inda mutumin yake, ya daure masa raunukan da aka ji masa, yana shafa masu mai da ruwan inabi. Ya dora shi a kan dabbarsa ya kawo shi wurin kwana, ya kula da shi
35 Washegari ya kawo dinari biyu, ya ba mai wurin kwanan ya ce 'Ka kula da shi, idan ma ka kashe fiye da haka, idan na dawo zan biya ka.'
36 A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?”
37 Sai malamin ya ce, “Wannan da ya nuna masa jinkai” Sai Yesu yace masa, “Ka je kai ma ka yi haka.”
38 Sa'adda suke tafiya, sai ya shiga cikin wani kauye, sai wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.
39 Tana da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kafafun Ubangiji tana jin abin da yake fadi.
40 Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, “Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni.”
41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, “Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa,
42 amma abu daya ne ya zama dole. Maryamu ta zabi abu mafi kyau, wanda ba za a iya kwace mata ba.”