13
1 A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu.
2 Sai Yesu ya amsa masu yace “Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka?
3 A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu.
4 Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5 Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka”
6 Yesu ya fada wannan misali, “Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba.
7 Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, “ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza?
8 Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki.
9 In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!”'
10 Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci.
11 Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa.
12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta.”
13 Sai Yesu ya dora hannunsa a kanta, nan da nan sai ta mike a tsaye ta fara daukaka Allah.
14 Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba.”
15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci?
16 Ashe wannan 'yar gidan Ibrahim, wanda shaidan ya daure ta shekara goma sha takwas, wato ba za a iya kwance ta a ranar Asabaci kenan ba?
17 Da ya fada wadannan abubuwa, dukansu da suka yi adawa da shi suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwa masu daraja da yayi.
18 Sai Yesu ya ce, “Yaya za a misalta mulkin Allah, kuma da me zan kwatanta shi?
19 Yananan kamar kwayar mastad, wanda wani mutum ya dauka ya jefa ta a lambunsa, ta kuma yi girma ta zama gagarumin itace, har tsuntsaye suka yi shekarsu a rassanta.”
20 Ya sake cewa, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
21 Yana kamar yisti wanda wata mace ta dauka ta cuda da mudu uku na garin alkama don ya kumburar da shi.”
22 Yesu ya ziyarci kowanne birni da kauye, a hanyar sa ta zuwa Urushalima yana koyar da su.
23 Sai wani ya ce masa, “Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?” Sai ya ce masu,
24 “Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa, domin na ce maku, mutane dayawa za su nemi shiga amma ba za su iya shiga ba.
25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.'
26 Sannan za ku ce, 'Mun ci mun sha a gabanka, ka kuma yi koyarwa a kan titunanmu.'
27 Amma zai amsa ya ce, “Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!'
28 Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje.
29 Za su zo daga gabas, yamma, kudu, da arewa, za su ci a teburin abinci a mulkin Allah.
30 Ku san da wannan, na karshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na karshe.”
31 Nan take, wadansu farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ka tafi daga nan domin Hirudus yana so ya kashe ka.”
32 Yesu ya ce, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.'
33 Ko da kaka, dole ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don bai dace a kashe annabi nesa da Urushalima ba.
34 Urushalima, Urushalima masu kisan annabawa, masu jifan wadanda aka aiko gare ku. Sau nawa ne ina so in tattara 'ya'yanki kamar yadda kaza take tattara 'ya'yanta a cikin fukafukanta, amma ba ki so wannan ba.
35 Duba, an yashe gidanki. Ina kwa gaya maku ba za ku kara ganina ba sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.'”